Manhajar Inganta Kiwon Kaji a Lokacin Dumamar Yanayi (Better Poultry Management Practices with Changes in Climate)

 

Feed the Future Innovation Lab for Food Security Policy

Nigeria Agricultural Policy Project & Alliance for African Partnership Nuwanba 2018

 

         


Me ake Nufi da Dumamar Yanayi?

Dumamar yanayin Duniya wani sauyin yanayi ne da ake shiga a wani lokaci da ke haifar da karancin ruwan sama da bazara mai nisa, wanda kuma yake haifar da yanayin zafi. Ko da yake ba a nan take ake la’akari da dukkanin sauyin yanayin da ke faruwa ba, amma kuma sai bayan lokaci mai tsawo ne za’a fuskanci illar da sauyin yanayin

 Wacce Illa Dumamar Yanayi Yake yi wa Gonakin Masu Kiwon Kaji?

Dumamar yanayi dai za’a iya danganta shi ne da karuwar zaf iga kajin da ake kiwo a gonaki. Wannan na nufin tsananin zafi fiye da wanda aka saba gani a lokuta mabanbanta. Tun kaji kan rage cin abinci a lokutan zafi, ka ga wannan zai shafi abin da ake sa ran samu daga kajin da ake kiwo kenan; zai shafi girmansu, zai shafi yawan tsoka da kwai da za’a samu da kuma yawan kamuwa da cututtuka saboda karancin sinadarai masu bayar da garkuwa ga lafiyar jiki. Yanayin dumamar yanayi na haifar da karuwar zafi da ke haura ma’aunin zafi digiri 30 na kalsiyos. Duk wannan na haifar da raguwar nauyin kaji da karuwar mutuwarsu. Kuma idan makiyayi ya lura zai ga idan ruwan sha kaji yayi zafi, za su rage shan ruwa da cin abinci mai yawa. Yanayin kuma zai rage yawan kwai da kananan kaji gidan gona (naTurawa). Bugu da kari, karuwar yanayin zafi na haifar da cututtuka, wanda ke saka gonakin kaji da dama cikin hatsari saboda yawaitar mutuwar kajin da raguwar amfanin da kajin ke samarwa ta hanyar kwai da Nama, wanda kuma a karshe manomi ko makiyayi ne ke fuskantar wannan asara.

 To, Mene ne abin yi a Gonakinmu Yanzu?

Albishirinku! Akwai matakai na kan-da-garki ko riga-kafi da ya kamata mai kiwon kaji ya dauka a gonakin kaji domin rage mutuwa ko asararsu da ake kiwo sakamakon karuwan zafi. Akwai bayanai da muka gabatar wa

makiyaya kamar ku a taruka daban-daban da ziyarceziyarcen da muka kai gonakinsu a baya. Wasu daga cikin masu kiwon kajin sun nuna mana matakan da suke dauka domin kare kajinsu daga illar dumamar yanayi, ko sauyin yanayi, domin rage asarar kajinsu, kuma muna shawartar ku, ku dauki irin wadannan matakai. 

 


 
Ta Yaya Za’a Rage Illar Zafi a kan Kajin da ake Kiwo?

1) A rage kiwon kaji masu duhu ko bakake domin zafi na saurin shigarsu.

2) Samar da kafofin iska wadatacciya a dakunan kaji

3) Idan da hali a kara yawan kajin da ake kiwo irin su ‘yar shika rowan kasa da nau’in FUNAAB alpha (‘yar Abekuta), ko kuma fararen kaji da masu haske domin zafi baya saurin shigarsu.

 


 

 

Ta Yaya mai Kiwo zai Samar da Yanayi mai Sanyi da Ruwan sha mai Sanyi ga Kajinsa a Lokutan Zafi ?

1) A dasa bishiyoyi musanman itacen ayaba domin ba da inuwa ga kaji.

2) A yawaita share gidan kajin akai-akai don rage yawan gurbatacciyar iska saboda kashin da suke yi.

3)  Lura da saka ido a kan kajin da ake kiwo da kuma tabbatar da yawansu ba zai hana su samun wadatacciyar iska da kuma walwala ba. Wato dai a rage yawan kaji a kowane gida ko akurki ko akurki ko filin kiwon.

4) Amfani da kwan fitila mara zafi domin rage zafi a dakin kaji.

5) A yawaita bai wa kajin nau’in maganin bitamin C da ruwa mai dauke da sinadarin tonic ko kuma binne hanyar ruwa a kasa domin su ji sanyi.

6)  Idan kuma kana tunanin fara kiwon kifi da sauran halittun ruwa hakan zai taimaka wajen samar wa kajin ruwa mai sanyi idan ka gina shi kusa da gidan kajin.

7) Matakan riga-kafi na da muhinmanci idan aka bi tsarin alluran riga-kafi da kuma samar da magunguna akai-akai.

8) Za a iya yayyafa musu ruwa akai- akai domin rage zafi.

9)  Idan kana amfani da tankin ruwa a kodayaushe zaka iya zubar da ruwan da ya yi zafi, a maye shi da mai sanyi da ga rijiyar burtsate ko rijiyar gargajiya kafin a shayar da kajin. Shayar da kajin ruwa mai sanyi yana kara yawan abincin da suke ci.

10) Za ka iya kafa tankin ruwan a cikin gidan kajin domin rage zafin rowan. 

11) Idan rowan ya yi zafi za ka iya saka kankara domin sanyaya shi.

12) Ciyar da kaji abinci sa’o’i hudu zuwa biyar kafin zafin rana ya tsananta zai taimaka wajen narkewar abincin a cikinsu, wanda hakan zai taimaka wa kajin su girma yadda ya kamata.

13)  A bai wa kaji maganin zafi akai-akai domin rigakafi.

 Wane Tanadi mai Kiwon Kaji ya Kamata ya yi Domin Gaba ?

1) Bayan daukar matakai ko shawarwarin da aka lissafa a gaba, mai kiwon kaji ya kamata ya yi la’akari da matakai na kimiya dake da alaka da sauyin yanayin duniya musanman ta bibiyar matakai da shugabannin duniya ke tattaunawa akai-akai na makomar duniya muddin aka kasa samun mafita bai-daya a irin wadannan taruka na duniya.

2) Idan kana da niyar gina gidan kaji ne, dole a ringa la’akari da matakan inganta gidannkaji. Tun Rana na fitowa ne ta Gabas ta fadi Yamma, saboda haka idan za a gina gidan kaji kafofin samar da iska ko tagogi su kalli Kudu da Arewa.

3)  Wannan zai rage zafin rana da zai shiga gidan kaji domin sanyaya dakin kajin.

4) A tabbatar rufin gidan kajin ya yi nisa da kasa sosai, kuma katangar da ta kewaye gidan kajin ba ta da tsawo domin samun wadatacciyar iska.

5)  Kimanta yawan kaji a kowane gidan kaji ko akurki bisa la’akari da lokacin zafi.

A karshe idan gidan kajinka na nesa ne ko kana da wadataccen fili za ka iya kewaye shi da katangar waya, maimakon gine shi da bulo domin kajinka su samu wadatacciyar iska mai lafiya. Amfani da kwanon rufi na alminiyon ko asbestos wajen rufin gidan kajin zai fi maimakon amfani da kwanon rufi na zink domin shi yana daukar zafi fiye da su. Haka kuma za a iya amfani da fanka domin samar da iska a dakunan kajin. 


 

 Domin karin bayani a tuntubi…Dr. Kazeem Bello (Federal University of Agriculture, Abeokuta kazeembello19@gmail.com (+2348032204658), or Dr. Buba Wahe, NAERLS, Ahmadu Bello University Zaria, bubawahe@gmail.com (+234806539885), Dr. Toba Adeyeye +2348083058853 or Dr. Saweda Onipede Liverpool-Tasie, Michigan State University, lliverp@msu.edu. Translated by Mr. Babangida Jibril, Hausa Service of the Voice of America VOA Wannan kasidar ta hadin guiwa ce ta wasu kwararru a kan illar sauyin yanayi da samar da abinci tare da hadin guiwar shirin samar da wadataccen abinci na GwamnatinTarayyar Nijeriya wato Feed the Future Nigeria Agricultural Policy Project da shirin Alliance for African Partnership na Jami’ar Jihar Michigan ta kasarAmurka.


Comments

Popular posts from this blog

Competitiveness and Comparative Advantage of Rice Production Systems: The Policy Analysis Matrix Approach